Rikicin siyasar Afirka ta Kudu na kara dagulewa | Labarai | DW | 04.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasar Afirka ta Kudu na kara dagulewa

Babbar kungiyar kwadagon Afirka ta Kudu ta bukaci Shugaba Jacob Zuma ya ajiye madafun iko sakamakon rudanin siyasa da shugaban ya janyo.

Kungiyar kwadagon kasar Afirka ta Kudu mai karfin fada aji, Cosatu, da ke zama babbar abokiyar kawance jam'iyyar ANC mai mulki, ta bukaci Shugaba Jacob Zuma ya ajiye madafun iko, sakamakon garambawul da ya yi wa majalisar zartarwa da ya haifar da cece-kuce. Sakataren kungiyar Bheki Ntshalintshali ya fadi haka. Ita wannan kungiya ta Cosatu tare da jam'iyyar ANC suka jagoranci gwagwarmaya bisa kawo karshen gwamnatin nuna wariyar launin fata ta Turawa tsiraru.

Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu ya shiga tsaka mai wuya tun lokacin da ya sallami tsohon ministan kudin Pravin Gordhan mutumin da ake girmamawa a ciki da wajen kasar. Akwai jiga-jigan jam'iyyar ANC mai mulki da suka soki matakin Shugaba Zuma.

Tuni sabon ministan kudin na Afirka ta Kudu, Malusi Gigaba wanda nada shi ya kawo rudani, ya yi alkawarin zai dauki matakai cikin gaggawa domin bunkasa tattalin arzikin kasar.