Rikicin siyasa ya kara cabewa a kasar Kote Divoire | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa ya kara cabewa a kasar Kote Divoire

A yayin da ranar 31 ga watan Oktber, ke gabatawa,. Wace itace,ranar karshe, ta wa´adin mulkin shuagaba Lauran Bagbo, al´umomin kasar Kote Divoire, sun kara shiga wani hali na rudani da zullumi.

A jiya, kungiyar yan tawayen FN ta hiddo sanarwa, inda ta jaddada cewa, daga wannan rana, ta litinin mai zuwa, sam, ta kare daukar Bagobo a matsayin shugaban kasar Kote Divoire.

Idan ba a manta ba, komitin sulhu na majalisar Dinkin Dunia bisa shawara kungiyar taraya Afrika, ya baiwa Bagbo, damar ci gaba da mulkin kasa, har tsawan wani saban wa´adi na watani 12 kamin a shirya saban zabe, matakin da yan tawaye su ka yi watsi da shi.

Shugaban kungiyar yan tawaye Guillaumwe Soro, ya bukaci majalisar ta amince yan tawaye su nada Praminista, saidai ya zuwa yanzu ba samu ba biyan bukata.

Su ma gugun jam´iyun adawa da ke nuna goyan bayan ga yan tawayen sun bukaci a nada daya daga cikin shuwagabanin su a matsayin saban praminista.

Saidai masu kulla da harakokin siyasa a kasar na nuni da cewa dalili da rashin cimma daidaitom tsakanin bangarorin daban daban akwai alamunPraminista mai ci yanzu Seydu Diara ya ci gaba da rike matsayin sa.