1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali: Rikicin siyasa wata biyu kafin zabe

Salissou Boukari
June 4, 2018

Ana cigaba da samun tashin jijiyoyin wuya tsakanin gwamnati da 'yan adawa a kasar Mali yayin da ya rage wata biyu a kai ga zaben shugaban kasa, bayan da 'yan adawa suka yi zargin harbinsu da harsashi na gaskiya.

https://p.dw.com/p/2ysx2
Mali | Proteste in Bamaku gegen die Intransparenz der Präsidenschaftswahlen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Cattani

 'Yan adawan na Mali dai sun zargi jami'an da ke tsaron lafiyar firaministan kasar da yin amfani da harsashi na gaskiya kan masu zanga-zanga a Bamako babban birnin kasar yayin da Firaministan ke ficewa, wanda ya yi sanadiyyar raunata mutane 25 a cewar wata majiya ta babban asibitin birnin.

Sai dai tuni Firaministan kasar ta Mali Soumeylou Boubeye Maïga, ya karyata zargin na 'yan adawa na cewa jami'an da ke bashi kariya sun yi amfani da harsashi na gaskiya wajen tarwatsa masu zanga-zanga, wanda ya ce kawai mataki ne na neman yawo da hankalin 'yan kasar ta Mali.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, da ya kai wa sojojinsu na MINUSCA da ke a kasar ta Mali ziyara a makon da ya gabata, ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun tashe-tashen hankula na siyasa a kasar ta Mali 'yan watanni kafin zabe.