1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Zimbabwe.

Zainab AM Abubakar.March 5, 2004
https://p.dw.com/p/BvlT
Yan sandan kwantar da tarzoma a Zimbabwe.
Yan sandan kwantar da tarzoma a Zimbabwe.Hoto: Ludger Schadomsky

Yanayi da ake ciki a Zimbabwe ayanzu haka na nuni dacewa Sojin kasar sun shiga sawun gaba na ganin cewa daya daga cikinsu ya maye gurbin mataimakin shugaban kasar,da halin yanzu babu kowa.idan har suka cimma wannan buri ,tsohon general na Sojin kasar zai shiga jerin wadanda zasu gaji Mugabe.

A yanzu haka dai wani tsohon Brigadier ke shugabantar hukumar leken asiri na kasar,ayayinda biyu daga cikin manyan Alkalan kasar tsoffin Soji ne,kana daya daga cikin gwamnonin kasar 8 shima ya kasance tsohon General na Soji ne.Baya ga wannan akwai mukamai kamar na sakataren maaikatar sufuri,shugaban hukumar samarda hatsi da harkokin ciniki,da kuma babban jamiin dake lura da gidajen yarin kasar,wadanda duk suka kasance tsoffin sojojin Zimbabwe.

A garon bawul da yayiwa maaikatun kasar a watan daya gabata shugaba Robert Mugabe ya nada sojoji hudu zuwa matakan minista da kuma mataimaki.

Manazarta dai sun bayyana cewa Mugabe nada dalilansa na nada tsoffin sojojin kasar zuwa muhimman mukamai a inda ya kamata ya kasance fararen hula ne.,inda sukace bazai kasa nasaba da burinsa na siyasa ba.A ranar jajiberin zaben shugaban kasa a shekarata ta 2002,manyan jamian sojin kasar sun fidda wata sanarwa dake nuni dacewa,su bazasu marawa mutumin da ya gaza yancin yaki ba,abun nufi anan shine shugaban jammiyar adawa Morgan tsivangirai.A watan Disamban shekarar data gabata ne Hafsan Sojin kasar ya sake nanata wannan matsayi na rundunar kasar.

Wani manazarci kann harkokin siyasa dake jamiar kimiya da fasaha,Themba Dlodlo yace mugabe na laakari ne da lokacinsa nayin murabus.Domin cimma nasaran zama cikin kwanciyan hankali bayan yayi Ritaya,Mugabe na bukatar wadannan Sojojin a manyan mukamai na kasar,tunda bazasu binciki miyagun ayyuka da yayi lokacin mulkinsa ba,saboda Uban gidansu ne.

Su kuwa yan adawa ,basu kasa bayyana damuwansu ba dangane da wannan tsari na shugaba Robbert Mugabe.Inda sukace ba karamin matsaloli kasar zata cigaba da kasancewa ciki ba sakamakon hargitsa mukamai tsakanin Sojoji da fararen hula.

Tun a shekarata 2000.zimbabwe ke fama da matsaloli na yunwa,wanda aka danganta da tsarin gwamnatin kasar na kwace gonaki daga fararen fata domin rabawa bakaken fatun kasar.Rahotanni dai sun tabbatar dacewa manyan Jamian gwamnatin kasar ne ke cin moriyar wannan tsari,ayayin matsaloli na rashin ayyukanyi da tattalin arziki ke dada tabarbarewa.

A dangane da hakane yan adawan kasar sukace,idan har sojoji na iya harba bindiga da gurneti saboda suna da horon haka,bazasu iya jagorantan mukamai na fararen hula ba tunda baa basu horo ta wannan bangare ba.Inda sukayi nuni dacewa wannan gwamnati ce ta tilas,wadda ke bukatar gudanarwa da tilas,kuma babu inda zai kai Zimbabwen sai dai dada durkusar da ita.