Rikicin siyasa a Ukraine ya dauki sabon salo | Labarai | DW | 26.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Ukraine ya dauki sabon salo

Dakarun dake biyyya da shugaban Ukraine Viktor Yuschchenko sun yi kokarin shiga Kiev babban birnin kasar a yau asabar bayan an dakatar da tattaunawar warware rikicin siyasar kasar da ake yi tsakanin shugaban da FM Viktor Yanukovich. Da farko an shirya komawa ga tattaunawar yau a wani mataki na gano bakin zaren warware dambarwar siyasar da ta ke barazanar gurgunta kasar. A halin da ake ciki Jamus ta bi sahun Rasha wajen yiwa shugabannin Ukraine kashedi da ka da su yi amfani da karfi wajen warware wannan rikici. Gwagwarmayar rike madafun iko tsakanin shugabannin biyu ta yi tsanani a jiya juma´a lokacin da shugaba Yushchenko ya karbi ikon dakarun ma´aikatar cikin gida.