Rikicin siyasa a Turquiyya
May 6, 2007Ministan harakokin wajen ƙasar Tukiyya, bugu da ƙari ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa, ya ga samu ya ga rashi.
Jam´iyar AKP ce,mai riƙe da ragamar mulki, ta ajje takara Abdallah Gul, gaban majalisar dokoki, amma duk da rinjaye ta, zaɓen ya gagara.
A zagayen farko, na ranar 27 ga watan Aprul, Kotin ƙoli ta rushe zaɓen, dalili da rashin samun issasun yan majalisa a lokacin kaɗa ƙuri´a.
Bisa dokokin tsarin mulkin ƙasar Turkiyya, cilas !!! sai a ƙalla kashi 2 bisa 3, na yan majalisa sun yi zaɓe, kamin ya sa mu karɓuwa.
Yau ne lahadi a ka buƙaci shirya zagaye na 2, amma shugaban majalisar ya tada taron, dalili da rashin samun addadin yan majalisar da ya cencenta.
Cemma kamin zaɓen jam´iyun adawa, sun ambata ƙaurace masa.
A hira da yayi da manema labarai, Abdallah Gul,ya ce zai janye takara sa, muddun bai ci nasara ba a zaɓen na yau.
Wannan zaɓe ya saka Turkiya a cikin wani hali na rikicin siyasa, wanda a sakamakon sa,gwamnati ta yanke shawara shirya zaɓen majalisar dokoki,na kamin lokaci, ranar 22 ga watan juli, tare da ɓullo da wasu dokokin kwaskarima, ga kundin tsarin mulki na ƙasa.