1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siyasa a tsakanin magabatan Somalia

Zainab A MohammadJune 7, 2005

Barkewan rikici a garin Baidoa a somalia

https://p.dw.com/p/BvbS
Hoto: AP

Gwamnatin shugaba Abdullahi Yusuf na Somalia dake gudanar da mulki daga birnin Nairobin kasar Kenya ,na muradin mayar da headquatanta a garin Baidoa,mai tazarar km 220 kudu maso yammacin fadar kasar dake birnin Mogadisho,ko kuma Jowhar mai tazar km 90 arewacin Mogadisho.

Gwamnatin Somalia dai akarkashin shugaba Yusuf nada goyon baya kalilan ne daga fadar kasar dake birnin mogadisho ,wanda ke hannun dakaru,wanda amadadin hakan ne yake muradin kasancewa a garuruwan Baidoa ko kuma jowhar,na wucin gadi kafin a kamala kwance damarar yaki tare da tabbatar da tsaro a wannan kasa.

To sai dai yan majalisar dokokin kasar wadanda suka fito daga Mogadisho na adawa da wannan raayi na shugaban kasa,inda suke neman bin kaidojin kundun tsarin mulkin kasar na cigaba da kasancewar fadar gwamnati a birnin Mogadisho.

A birnin Nairobin kasar Kenya nedai aka nada gwamnatin rikon kwarya na Somalia tun a farkon wannan shekara sakamakon,tsoron rikici da wannan kasa ke fama dashi na lokaci mai tsawo.

To sai dai a farkon wannan mako da muke ciki nedai fada ya barke a garin Baidoa,wanda ya dada kawo sabanin raayi tsakanin magabatan kasar dangane da inda zai kasance matsugunin gwamnati.

A wannan fada dai kimanin mutane 13 suka rasa rayukansu ayayinda wasu 29.Wannan rikici dai ya dada tayar da hankalin mazauna wannan yankin a wannan kasa data fada rikicin siyasa tun bayan gwamnatin dan mulkin kama karya mohammad Siad Barre a shekarata 1991.

Tun daga wannan shekara ne shugabannin hauloli ke jan ragamar mulkin Somalia,inda a wasu bangarori suka sanar da yancin kai alal misali yankin arewa maso gabashi dake Puntland,wadda ayanzu ke gudanar da harkokinta,ayayinda Somali land dake karkashin mulkin mallaka na Britania a baya ,wadda kuma ta hade da sauran sassan Somalia a shekarun 1960,ke neman ayi mata kallon yantacciyar kasa.

Bayan barkewan fadan na garin Baidoa dake karkashin Dan majalisa Mohammad Ibrahim Habsade,an kuma samu hare hare na dakaru dake marawa ministocin kasar biyu dake marawa shugaba Yusuf baya dangane da sauya matsugunin gwamnati zuwa wannan gari na Baidoa.Ayayinda Dan majalisa Habsade ke ganin cewa idan fadar gwamnati ta koma nan,zai rasa madafan ikonsa.

A yanzu haka dai manazarta na ganin cewa wannan sabanin raayi dake gudana tsakanin magabatan Somalia dangane da sauya matsugunin gwamnati daga Mogadisho zuwa garin Baidoa,zai iya haifar da jinkiri wajen kaurar da gwamnatin daga birnin Nairobin Kenya zuwa cikin Somalia.

Tattaunawa kan wannan batu a watan Maris dai ya haifar da doke doke tsakanin yan siyasar kasar a Birnin Nairobi,inda kowa ya samu rabonsa da dambe ko kuma jifan kujera.a birnin Nairobi.

Gwamnatin Somalian dai a yanzu haka na tattaunawa da kungiyar gamayyar Afrika Au ,dangane da yiwuwar tura ayarin dakarun kiyaye zaman lafiya zuwa sabon fadar mulkin kasar idan har ya tabbata.