Rikicin siyasa a Sudan | Labarai | DW | 21.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Sudan

Mataimakin shugaban ƙasar Sudan Ali Usman Taha, yayi kira ga tsafin yan tawayen kudancin ƙasar, su koma kan kujerun su, a majalisar gwamnati, da su ka ƙauracema makon da ya gabata.

A cewar Ali Usman Taha, babu cikkakar hujar ɗaukar wannan mataki, ta la´akari da cewar, gwamnati ta cika mafi yawa daga alƙawarun da ta ɗauka a lokacin da ta rattaba hannu a kan yarjejiya da yan tawayen mirganyi John Garang.

A ɗaya rikicin na ƙasar Sudan, Majalisar Ɗinkin Dunia ta yi kira ga ƙasashe masu hanu da shuni, su taimaka da jirage masu dura angulla ga rundunar kwantar da tarzoma da ta ke shirtinaikawa a yankin darfur.

A yayin da ya rage yan kwanaki ƙalilan a aika wannan runduna, har yanzu babu ƙasar da ta bada gudumumuwar irin wannan jirage.