1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Somalia

Zainab A MohammadSeptember 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bty0
Zanga zangar mata a Kismayo,Somalia
Zanga zangar mata a Kismayo,SomaliaHoto: AP

Ministan harkokin waje na gwamnatin rikon kwarya a Somaliya,yayi kira ga komitin sulhun majalisar dunkin diniya,daya dage takunkumin makamai na tsawon shekaru 14 da aka kakabawa kasarsa dake fama da rashin tsaro,domin bawa dakarun kiyaye zaman lafiyan ketare daman shiga kasar.

Ismaila Hurreh ya fadawa zauren mdd cewa ,ya zamanto wajibi komitin sulhu ya sake nazari kann wannan takunkumi,domin samarwa alummar wannan kasa zaman lafiya.

Bugu da kari yayi kira da bukatar a tura dakarun kiyaye zaman na kungiyar gamayyar Afrika,shirinda gamayyar kotunan musulmi sukayi adawa dashi.

Kungiyar lura da harkokin mulki a kasashen gabashin Afrika mai wakilan kasashe 7,IGAD a takaice ta amince da shirin tura dakarun kiyaye zaman lafiya kimanin dubu 8,domin taimakawa harkokin tsaro a wannan kasa.

Gamayyar kotunan Islaman dai sun dakatar da wata zanga zangar mata a garin kismayo dake daya daga cikin manyan tashoshin jiragen ruwa dake kudancin somaliyan,tare da sanya dokar haramta fita sakamakon bore na adawa da mamayen garin da mayakan kungiyar sukayi.

Yini guda bayan karban madafan ikon wannan gari na kismayo cikin lumana nedai,alummominta suka gudanar da wani gagarumin zanga zanga,wanda kuma yasa mayakan gamayyar kotunan islaman suka buda wuta,wanda yayi sanadiyyar mutuwan wani matashi mai shekaru 13 da haihuwa.Bayan nan ne aka kafa dokar hana fita daga karfe 9 na maraice zuwa biyar na safiya a Kismayo.

To sai dai a nasu bangare gamayyar kotunan islaman sun hakikance cewa sun mamaye wannan gari ne bisa ga bukatun alummominta.kamar yadda mataimakin babbasn jamiin kula da harkokin ketare na kungiyar yayi nuni dashiMohammed Ali Ibrahim.

Kismayo na mai kasancewa wuri mafi girma da kotunan Islaman suka kama madafan ikonsa,tun bayan kwace birnin Mogadisho daga hannun shugabannin hauloli dake da goyon bayan Amurka,a watan yuni.

Kasancewar Somaliyan na cigaba da wadannan rigimu,wadda zaa iya kwatantawa da kasar Afganistan,inda ake zargin yan Taliban da adawa da democradiyya,shin ba abunda zai kasance da wannan kasa ba kenan.

Ministan harkokin wajen somaliyan yayi amfani da zauren mdd wajen kira ga kasashen duniya dasu nuna halin sanin yakamata,wajen tallafawa kasarsa a siyasance da kudade da inganta harkokin fasaha,musamman domin tallafawa gwamnatin rikon kwarya,da a halin yanzu keda madafan iko a wurare kalilan a wannan kasa.

Kazalika Ismael Hurreh yayi kira da agajin gaggwa wa yan somaliya kimanin 1.8 dake bukatarsa.