1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siyasa a Nijeriya

February 8, 2010

Ana fama da rikicin siyasa a Nijeriya sakamakon rashin lafiyar shugaba Umaru Musa 'Yar Aduwa

https://p.dw.com/p/Lvp5
Shugaban Nijeriya Alhaji Umaru Musa 'Yar AduwaHoto: picture alliance/dpa

Bayan kammala gasar cin kofin ƙwallon ƙafa da aka kammala a ƙarshen makon da ya wuwuce a Angola, a wannan makon jaridun na Jamus sun mayar da hankalin su ne akan al'amuran siyasa a sassa daban-daban na nahiyar Afirka. Misali jaridar Die Tageszeitung ta leƙa Nijeriya, ƙasar da ta ce a halin yanzu gangar jiki ce kawai ba kai, tana mai hannunka mai sanda a game da rashin lafiyar shugaba Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa, wanda take gani shi ne ummalaba'isin rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a makekiyar ƙasar ta yammacin Afirka. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"A halin yanzu ƙungiyoyi masu zazzafan ra'ayi na Islama da 'yan tawayen Niger Delta sun samu ƙwarin guiwa sakamakon rikicin siyasar da Nijeriya ke fama da shi tun bayan rashin lafiyar shugaban ƙasar Alhaji Umaru Musa 'Yar Aduwa. Ƙungiyar Mend, a karo farko ta fito fili tana mai nuna shirinta na kai hare-haren ta'addanci a wajen yankin Niger Delta, sannan ita kuma ƙungiyar al-ƙa'ida ta Maghreb tayi wa 'yan-uwanta a Nijeriya tayin ba su taimako horo da makamai. Dukkan waɗannan abubuwa na yin nuni ne da mawuyacin hali na tsaro da Nijeriya ta samu kanta a ciki yanzun."

A cikin wata sabuwa kuma a wannan makon kutun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka dake birnin The Hague ta bayyana shirinta na ƙara wasu zarge-zarge akan shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir. A lokacin da take ba da rahoto jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

Omar Hassan Ahmad al-Bashir Präsident Sudan Internationalen Strafgerichtshof Logo
Shugaba Omar Al-Bashir na SudanHoto: picture-alliance/dpa/Montage DW

"Bisa ga ra'ayin mai ɗaukaka ƙara a kotun ƙasa da ƙasa akan miyagun laifuka dake The Hague, shugaba Omar al-Bashir na da alhakin kisan aƙalla mutane dubu talatin da biyar a yankin Darfur tsakanin shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2005. A dai watan maris na shekarar da ta gabata ne kotun ta The Hague ta tsayar da shawarar ɗaukaka ƙara kan shugaban na Sudan game da laifin cin mutuncin ɗan-Adam. Kuma tun a wancan lokaci ne mai ɗaukaka ƙarar Luis Moreno Ocampo ya nema da a haɗa da laifin kisan kiyashi, amma ba a amince da hakan ba."

Wani nazari da aka yi ya gano cewar ƙasashen Afirka zata iya fuskantar matsaloli na koma bayan al'amuran kiwon lafiya da ilimi da daidaita cinikayyarta da sauran sasa na duniya, sakamakon watsi da aka yi da waɗannan batutuwa a fafutukar da ake yi wajen yaƙi da ɗimamar yanayi, jaridar Süddeutsche Zeitung ce ta rawaito wannan rahoton tana mai danganta shi da sakamakon nazarin da wata cibiyar Birtaniya mai suna Overseas Development Institute ta gudanar baya-bayan nan.

A wannan makon ba zato ba tsammani hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasashen Afirka ta gabatar da wata zartarwar dake cewa wai an dakatar da ƙungiyar wassan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Togo daga shiga gasar ƙwallon ƙafa ta cin kofin ƙasashen Afirka har sai bayan shekaru shida masu zuwa saboda ƙin shiga wasannin na bana da tayi sakamakon harin da aka kai kan 'yan wasanta aka kuma halaka mutane biyu. Jaridar Die Welt ta bayyana mamakinta game da wannan zartaswa, inda ta ce:

"Ko da yake a cikin ƙudurin hukumar an tanadi cewar duk wata ƙasar da ta ƙin shiga wasannin da aka shirya ba a bisa ƙa'ida ba zata fuskanci irin wannan dakatarwa, amma kuma a ɗaya hannun ƙudurin kansa yayi nuni da cewar idan wata hukuma ce ta ba da umarnin irin wannan janyewa to kuwa babu laifi. Bugu da ƙari kuma su kansu jami'an hukumar ne suka yi wa 'yan wasan na Togo rakiya zuwa filin jirgin sama tare da nuna musu jajye ta la'akari dai da abin da ya faru wannan mataki da hukumar ta ɗauka ko kaɗan bata yi hangen nesa ba."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu