Rikicin siyasa a Nigeria | Labarai | DW | 18.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Nigeria

Jam´iyar PDP mai riƙe da ragamar mulki a Nigeria ta maida martani, ga kiran ƙawacen jam´iiyun adawa na ƙauracewa zaɓen shugaban ƙasa, ranar asabar mai .

Sakataran kula da hulɗoɗi ne da ƙetare, na jama´iyar PDPin , ya bayyan wannan sanarwa.

John Odey, yayi watsi da ƙorafe-ƙorafen jam´iyun adawa, na zargin PDP da tabaka maguɗi a zaɓen gwamnoni da yan majalisun jihohi, ramar assabar da ta wuce.

Wannan martani ya biwo bayan taron jam´iyun adawa 18, jiya talata a birninAbuja.

A sakamakon mahaurorinda su ka gudanar,jam´iyun 18,su bukaci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta soke baki ɗayan zaɓen da aka gudanar ranar assabar,sannan gwamnati ta russa hukumar zaɓen wato INEC da su ke zargi da zamam kariyar farautar shugaba Olesegun Obasanjo,,kazalika yan adawa sun bukaci dage ranar zaɓen shugaban ƙasar, tare da yin kira ga majalisar dokoki, ta kiri taro na mussamman, domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen da ya gabata.

Jam´iyun na adawa sun yi barazanar ƙauracewa zaɓen shugaban ƙasa na ranar assabar mai zuwa, muddun wannan sharuɗa basu cika ba.

Gobe alhamis idan Allah ya kai mu,jam´iyun za su sake saban taro, domin ci gaba da tantanawa, a game da baddaƙalar siyasa da ke wakana a taraya Nigeria.

Wannan cigulutun siyasa a Nigeria na wakana a yayin da a Kanon Dabo, a ke ci gaba da gurmuzu tsakanin rundunar tsaro ta ƙasa da wasu yan yaƙin sunkuru.