Rikicin siyasa a Nepal ya dauki sabon salo | Labarai | DW | 18.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Nepal ya dauki sabon salo

A yau aka shiga rana ta goma sha uku aci gaba da yajin aikin sai baba ta gani a kasar Nepal na adawa da mulkin sarki Gyanendra.

Yajin aikin da jamiyyun adawa na kasar suka kira, a yanzu haka ya haifar tsayuwar al´amurra cik a da yawa daga cikin birane na kasar.

Daga dai tun lokacin da aka fara yajin aikin ya zuwa yanzu an kiyasta cewa mutane biyar ne suka rugamu gidan gaskiya, a sakamakon dauki ba dadin dake wanzuwa a tsakanin masu zanga zanga da kuma jami´an tsaro na kasar.

Rahotanni dai na nuni da cewa masu zanga zangar na neman sarki Gyanendra sauka ne daga madafun iko na kasar , bisa zargi da suka yi masa na mulkin kama karya.