1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siyasa a kasar Cote Divoire

Yahouza sadissouSeptember 20, 2005

Shugaban kasar Kote Divoire Lauran Bagbo, ya gayaci shugaba Tabon Mbeki na Afrika ta kudu,dake shiga tsakanin rikicin kasar, da ya kiri wani saban taro

https://p.dw.com/p/BvZX

Burin da ya ke bukatar cimma shine na kayyade ranar da za a gudanar da zaben shugaban kasa, kasancewar zaben ba za shi yiwu ba,ranar 30 ga watan oktober, da a ka ambata da farko.

Bagbo ya rubuta wasika ga wakilin mussaman na majalisar Dinkin Dunia a Kote Divoire Pierre Schori, da kuma Antonio Montero, wakilin Koffi Annan, mai kulla da harakokin zabe a kasar,inda ya bayyana masu aniyar sa, ta shirya saban taro a birnin Yamuskuro.

Saidai kamar yada kila a ka riga aka sani, kungiyar tawaye ta FN, ta bayyana kawracewa shiga tsakanin Tabon Mbek,i bayan ta zarge shi, da nuna san zuciyya, da kuma goyan baya ga bangaren Lauran Bagbo.

Bayan wata ganawa da yayi, da shugaban kungiyar CEDEAO kokuma ECOWAS, bugu da kari shugaban Jamhuriyar Niger Tanja Mamadu, Guillaume Sorro ya bayana bukatar yan tawaye da wannan kungiya, ta karbi jagorancin sulhunta rikicin Kote Divoire daga hannun Tabon Mbeki.

A yayin da yake jawabi a Majalisar Dinkin Dunia ,shugaban kungiyar tayar Afrika, Olesegun Obasanjo, ya bayyana yiwuwar cenza sallon sulhunta rikicin, na Ivory Coast,abinda wasu su ka passara tamkar wata hanya ta kware baya, ga shugabn kasar Afrika ta kudu dake shiga tsakani.

Obasanjo ya tabatar da kungiyar taraya Afrika da ECOWAS, za su shawarci Majalisar Dinkin Dunia domi samun mafitar wanann rikici, da ya ki ci ya ki cenyewa.

Ya bukaci da su gayyato yan tawaye da jamiyun siyasa, domin a koma tebrin shawara, bisa jagorancin Shugaba Tabon Mbeki.

Lauran Bagbo, ya sanar da magoya bayan sa cewa, ya rubuta wasika zuwa ga sakatare Jannar na Majalisar Dunia Koffi Annan, domin sannar da shi, cewa shi fa ya cika dukkan alkawuran da ya dauka, a tarruka daban daban da su ka yi da yan tawaye da kuma jam´iyun siyasa.

Wata majiyar diplomitia ta bayyana cewa, nan da karshen watan da mu ke ciki, shugaban kingiyar taraya Afrika, za shi kiri taro na mussaman a birinin Abuja na Tarayya Nigeria, domin sake tantana batun rikicin kasar Kote Divoire.

A bayan sa kuma, za shirya wani zaman taro na kwanaki 15 a birnin Addis Abeba na kasar Habasha, wanda zai hada shuwagabani kasashenAfrika membobin komitin tabatar da zaman lahia, da na CEDEAO.

Mahimman wanan tarruka shine, na duba makomar siyasar kasar Kote Divoire, bayan ranar 30 ga watan Oktober, wace itace wa´adin karshe na mulkin shugaban Lauran Bagbo.

Kuma tunni ! yan tawaye da jamiyun adawa, sun bayana karrara, cewa daga wannan rana, sun daina daukar sa tamkar shuagaban kasa.

Sun bukaci girka gwamnatin rikon kwarya ,tare da maida Bagbo saniyar ware, matakin da shugaban kasar ya watsi da shi.