Rikicin siyasa a Jamus | Labarai | DW | 02.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin siyasa a Jamus

KO kamin ta kama aiki, sabuwar gwamnatin Angeller Merkel a nan Jamus ta shiga wani hali na rudani.

Shugabn jamiyar CSU mai kawance da CDU,Edmond Stoiber ya bayana murabus daga mukamin san a ministan tattalin arzikin, a cikin sabuwar gwamnatin ta hadin kai, tsakanin CDU-CSU da SPD.

Shikuwa shugaban jamiyar SPD Franz Münterfaring, ya sauzka daga wanna n matsayin bayan wata dambawar siyasa da ta kuno kai a jamiyar.

Ya zuwa yanzu, babu cikkaken tabas, a game da ko zai rike matsayin da a ka bashi, na mataimakin Angeller Merkel a cikin sabuwar gwamnatin.

KusoshinJam´iyar SPD, sun zabi Mathias Platzejk a matsayin saban shugaban jamiyar SPD, domin maye gurbin Franz Münterfering..

Komitin zartaswa na jam´iyar ya shirya wani zaman taro a yau, domin tantana matakan bullolwa saban rikicin da jamiyar ke fuskanta.

Haka zalika shugabar gwamnati, mai jiran gado Angeler Merkell ta jaddada aniyar ta, ta girka gwamnatin hadin gwiwa mai karfi duk da matsalolin da su ka kunno kai.