1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Cote Divoire

Yahouza sadissouAugust 30, 2005

Hadin gwiwar jam´iyun adawa sun bukaci a kaffa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Cote Divoire

https://p.dw.com/p/Bva7

A kasar Cote d´Ivoire kawancen jamiyun adawa sun bi sahun yan tawaye, inda su ka bukaci a girka sabuwar gwamnatin rikon kwarya, tare da mayar da shugaba mai ci yanzu, Lauran bagbo saniyar ware.

Girka sabuwar gwamnatin rikon kwarya ya zama wajibi inji jamiyun adawar Cote d´Ivoire, domin itace hanyar mafi inganci ta shirya zabe cikin tsabta da kuma, tanade- tanade na dokokin kasa, tare da sa hannun bangarori daban daban na siyasa.

Yan adawar, kamar yan tawaye, na zargin Bagbo da zama babban mai mayar da hannun agogo baya, a fadi ka tashin da a ke na shinfída zaman lahia a Cote d´Ivoire.

A game da zaben shugaban kasa, da a ka shirya yi ranar 30 ga watan oktober na wannan shekara, yan adawa sun bayyana cewa, a halin da ake ciki, babu alamun za a yi nasara shirya zaben a ranar da aka tsaida, dalili da, a zahiri, babu wasu mattakai masu kwari, na tabbatar da adalci.

A kan haka wajibi ne, inji hadin gwiwar jam´iyun adawa a tanadi wani sabuwar gwamnatin rikwan kwarya, daga ranar 30 ga watan oktober, wace ita ce ranar karshe, ta wa´adin Lauran Bagbo, a karagar mulkin kasar.

Saidai kuma, doli a mayar da Lauran bagbo saniyar ware, muddun a na da burin cimma zamman lahia a Cote d´Ivoire.

Hadin gwiwar jamiyun, mai suna gungun mabiya tafarkin Hufuwet Boiyi, wato RHDP a takaice, ya kunshi jam´iyar PDCI ta mirganyi Hufuwet Boiyi, wace kuma a hakin yanzu tsofan shugaban kasa Henri Konnan Bedie, ke jagoranta, da jam´iyar RDR ta Allasan Watara tsofan praminista, a zamanin Hufuweit.

Dukan shuwagabanin jamiyu 2 a yanzu haka, na cikin gudun hijira a kasar Fransa.

Dukkan a kwanaki da su ka gabata sun bayyana aniyar su ta shiga takara zaben, sun kuma yanke shawara gama karfi domin fuskantar jamiyar FPI ta Lauran Bagbo wadda a halin yanzu ke rike da raggamar mulki.

Sannan akwai wasu kanana jamiyun 2 dake basu goyan bayan sune, UDPCI da kuma MFA.

A nasa bangare shugaban Lauran Bagbo, ya tabbatar da ya na tsaye kan bakan sa, na shirya zabe ranar 30 ga watan oktober. Ya kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Dunia, da shugaba Tabon Mbeki na Afrika ta Kudu mai shiga tsakani ,da su yanke hukunci a game da wannan takkadama.

Lauran Bagbao ya yi watsi da bukatar yan tawaye, da yan adawa, ta sabka daga karaga mulki bayan 30 ga watan oktober.

Gobe ne idan Allah ya nuna manna, komitin sulhu na majalisar Dinkin dunia, zai zammna taro na mussaman, domin bayyana matsayin sa, a game da rikicin Cote d´Ivoire.

Taron zai samu halartar wakilin shugaban Tabon Mbeki, da kuma na tawagar majalisar Dinkin Dunia a kasar.