Rikicin siyasa a Burundi | Siyasa | DW | 24.08.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasa a Burundi

Al´ummar Burundi ta shiga halin ruɗani a sakamakon rikicin siyasa.

default

Ƙasar Burundi ta tsinci kanta cikin wani saban yanayin siyasa, mai cike da ruɗani, a sakamkon kame- kame, da gwamnatin ke ci gaba da yi , bayan abinda ta kira yunƙurin kifar da shugaba Pierre Nkurunzizia, wanda ya cika shekara ɗaya yanzu, bisa karagar mulki.

Kakakin jam´iyar adawa Uprona, ta yan tutsi zalla, Aloys Rubuka,ya ce bayan shekara guda da shugaban ƙasar yayi kan karagar mulki, yanayin zamantakewa ya ƙara taɓarɓarewa, ta hanyar gallazawa mutanen da baus ji bas u gani, tare da zargin tada hasumi, sannan tattalin arzikin ƙasa ya kai fagen lahaula.

To saidai kakakin gwammnati Burundi, Karenga Ramadhani, ya maida martani, ga wannan kalamomi, na yan tawaye da ya danganta da shirme.

A ta bakin Ramadhani, gwamnatin Pierre Nkurunziza, ta taka rawar gani, a tsawan shekara ɗaya kaccal ,da ta hau mulki ta la´akari da kyaukyawar nasara da ta cimma, ta fanin tabbatar da tsaro.

Saidai rahotani daga kasar na nunar da cewa, hankulla sun daɗɗa tashi, a Bujunbura da sauran biranen Burundi a farkon watan da mu ke ciki, bayan gwamnati ta bankaɗo wani yunƙurin juyin mulki.

Binciken da ta gudanar, ya gano cewar, tsofan shugaban ƙasa bugu da kari,jigo a jam´iyar adawa ta Frodebu, wato Domitien Ndayizeye, na da hannun cikin yunƙurin kifar da shugaban ƙasa.

A makon da ya gabata, Pierre Nkurunziza, ya gabatar da jawabi ga al´umma, inda ya bukaci a kwantar da hankula, sannan ya tabatar da cewa, gwamnati ta ɗauki matakan da su ka dace, domin fuskantar masu tada zaune tsaye cikin ƙasa.

Sakatare Jannar na Majlisar Dinkin Dunia Kofi Annan, ya bayana damuwa matuƙa ainun, da halin zullumin da a ke cikin yanzu a Burundi.

Ƙungiyoin fara hulla, jami´yun adawa, da rediyoyi masu zaman kansu, sun mussanta yuƙurin juyin mulkin da gwamnati ta ce, ta bankaɗo, a nasu gani wani sallo kaɗai na kauda yan adawa.

Itama ƙungiyar kare haƙƙoƙin jama´a, ta Human Rights Watch, ta soki gwamnatin Bujumbura, da tozartawa jama´ar ƙasa.

Wani jami´in diplomatia da ke babban birnin Burundi, ya tabatar da cewa, har yanzu gwamnati na da goyan bayan ƙasashen turai da Amurika, to saidai al´ammarin da ke wakana yanzu, na tada hankali opisoshin jikadancin da ke ƙasar.

Bayan shekaru 13, na yaƙe- yaƙen bassasa, Burundi ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, a watan Ogust na shekara ta 2005.

Sannan daga samun yancin ƙasar a shekara ta 1962 ta fuskanci juyin mulki da dama.

Don maida ƙasar bisa ingantacen tafarki na ci gaba, ƙasashe da ƙungiyin bada agaji na dunia, sun yi kira ga ɓangarori daban-daban masu gaba da juna, su bada fifiko ga tantanawa, domin warware rikicin wannan ƙasa.

 • Kwanan wata 24.08.2006
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtyY
 • Kwanan wata 24.08.2006
 • Mawallafi Yahouza S.Madobi
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BtyY