1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasa a ƙasar Tailand

Firaministan Tailand ya ɗage ranar zaɓe, matakin da ya ƙara rura wutar rikicin siyasar ƙasar.

default

Rikicin siyasar Tailand ya ƙara rincaɓewa

 Rikicin Ƙasar Tailand har yanzu yana  cigaba da rincaɓewa, sakamakon sake ranar zaɓen da Frime Ministan ƙasar Abhisit Vejjajiva ya yi daga watan Nuwamban bana.

Frime Ministan, ya ce ya soke ranar zaɓen ne saboda masu zanga-zangar sun ƙi su daina tashin hankalin da suke yi, kuma ya umurci jami'an tsaro da su tabbatar da cewa an kawo ƙarshen wannan rikicin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Kakakin  Frime Ministan kasar, Korbsak Sabhavasu ya yi bayyani kamar haka ya nha cewar:

Firaministan ya  shimfiɗa wa yan zanga-zangar wa'adi, amma sun ƙi aiki da shi. Saboda haka tayin da gwamnati tayi masu na gudanar da  sabon zaɓe ranar 14 ga watan Nuwamba babu shi a halin yanzu.

Masu nuna adawan sun cigaba da harbe-harbe a birnin Bankgok bayan da sojoji suka ce za su killace wurin da su ka kafa sansaninsu sa'an nan kuma a hana shiga da fita.

Ofisoshin jakadanci da dama sun dakatar da aiki, ofisoshin jakadancin Birtaniya da Amurka da na Holland sun daina ba da takardar izinin shiga Ƙasashensu, bayan da aka yi barazanan yanke wutan lantarki da ruwa.

Kakakin soja Sansern Kaewkamnerd  yace za'a ɗauki wasu matakai  domin ƙara matsa lamba kan ´yan zanga-zangar:

Akwai  al'amura da dama da tilas ne a kula dasu, idan har za'a katse wutar lantarki ko hanyoyin samar da ruwa. Yan zanga-zangar suna amfani da  na'urori na kansu domin samar da lantarki, suna kuma  samun ruwan da suke bukata daga  motocin kashe gobara. Idan har aka ci gaba da haka, al'ummar gari ne zasu  fi  shan wahala fiye da masu zanga-zangar.

Masu lura da al´amura sun ce akwai alamun cewa za'a sami rarrabuwan kawuna tsakanin masu tsatsaurar ra'ayi da masu matsakaicin ra'ayi a cikin masu zanga-zangar kuma idan har Frime Ministan bai bari an gudanar da zaɓen yadda aka tsara ba, zai fuskanci gagarumin rikici.

Bugu da ƙari kuma,  yan zanga-zangar suna ganin gwamnatin bata fito fili ta tabbatar da cewar  za'a rushe Majalisar Dokoki a lokacin da  aka ce za'a yi hakan ba. Gwamnatin tace idan duka ɓangarorin biyu  suka daidaita, za'a rushe majalisar dokokin daga tsakiyar watan Satumba. To sai dai wani mai zanga-zanga ya nuna shakkar sa, inda yace:

Firayim minista Abhist tun da farko,  bai fuskance mu da zuciya ɗaya ba. Mun nemi  a rushe Majalisar Dokoki amma ya ƙi  gaya mana  haƙiƙanin ranar da  za'a rushe ta, inda a maimakon haka, ya tsaida lokacin da za'a yi sabon zaɓe kawai, ko da shike yin haka baya ƙarƙashin ikon sa.

Masu sharaɗi dai sun ce gwamnatin Tailand tana cikin tsaka mai wuya.

Mawwallafi: Pinado Abdu Edita: Yahouza Sadissou Madobi