1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin shirin nukiliyar Iran

February 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9M
Shugaban Amirka GWB da sakatariyar harkokin waje Condoleezza Rice sun ce hukuncin da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta yanke na yin karar Iran a gaban kwamitin sulhu na MDD wata muhimmiyar manuniya ce ga gwamnatin Teheran. Bush ya ce duniya ba zata amince Iran ta mallaki makaman nukiliya ba. Bush ya kara da cewa shawarar mika Iran ga kwamitin sulhu shine matakin farko amma ba na karshe ba a kokarin bin hanyoyin diplomasiya don hana Iran din kera makaman nukiliya. Shi kuwa a lokacin da yake mayar da martani ga hukuncin na hukumar IAEA, shugaban Iran Mahmud Ahmedi Nijad ya ba da umarnin fara aikin sarrafa sinadarin uranium tare da katse duk wani hadin kai da ake bawa jami´an IAEA masu bincike na bazata a tashoshin nukiliyar Iran. Hukumomin Iran dai sun ce shirin su na nukiliya don samar da wutar lantarki ne amma ba kera makamai ba. A cikin watan maris kwamitin sulhu zai tattauna akan kasar ta Iran.