Rikicin shirin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 02.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin shirin nukiliyar Iran

A takaddamar da ake yi game da shirin nukiliyar Iran, an gabatar da sabbin shawarwari da nufin warware wannan rikici ta hanyoyin diplomasiya. A gun taron da suka yi a birnin Vienna ministocin harkokin wajen manyan daulolin kwamitin sulhun MDD hade da Jamus sun amince su dauki mataki na bai daya don tinkarar wannan batu. Sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Margaret Beckett ta ce za´a sakawa gwamnati a Teheran da abubuwa masu fa´ida idan ta dakatar da shirin inganta sinadrin uranium. Idan kuma ta ki to ta kwana da sanin cewa za´a dauki tsauraran matakai kanta. Kafofin yada labaru sun rawaito cewa an yiwa Iran tayin bata fasahar samar da makamashi ta zamani.