Rikicin Rasha da Georgia | Labarai | DW | 29.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Rasha da Georgia

Ministocin tsaro na NATO sun yi kira ga ƙasashen Rasha da Georgia su nuna halin dattaku, su sassauta taƙaddamar da ta kaure a tsakanin su bisa zargin leƙen asiri a tsakanin kasashen biyu. Babban sakataren ƙungiyar ta NATO Jaap de Hoop Scheffer, bayan ganawa da Ministan tsaro na ƙasar Rasha Sergei Lavrov, yace babu wata rawa da kungiyar kasancen zata taka a rikicin. Bayan ruɗanin da ya dabaibaye zargin leƙen asirin, an shiga tankiya da ƙaruwar fargaba tsakanin Mosco da Tbilisi saboda tattaunawa ta ƙarfafa danganta da ƙungiyar NATO ta shiga yi da Georgia wanda ka iya kaiwa ga shigar da Geogian cikin ƙungiyar. Fadar Mosco ta baiyana matakin da cewa wani yunkuri ne na haifar da ƙin jinin manufofin Rasha a Georgia. A waje guda kuma Rasha ta fara janye jamián ta daga ƙasar ta Georgia. An fara takun saka tsakanin Rasha da Georgia a ranar Larabar data gabata, bayan da Georgia ta kame wasu sojin ƙasar Rashan su hudu bisa zargin leken asiri. Tuni mahukuntan kasar suka gabatar da sojojin a gaban kotu a ranar jumaár nan jumaá domin fuskantar shariá.