Rikicin Rasha da Amirka ya kazanta
July 31, 2017Talla
Dama dai ma'aikatar harkokin wajen Rashar ta ce za a rage jami'an na Amirka 455 ne gabanin sanarwar ta shugaba Putin, a lokacin da majalisar dattawan Amirka ta amince da tsananta batun takunkumi ga kasar.
Dangantaka tsakanin Amirka da Rasha dai ta yi zafi ne bayan zaben Amirka da aka yi a bara, zaben da ake zargin Rasha ta yi kutse a cikinsa.
Shugaba Putin ya kuma ce kada a yi tsammanin samun daidaito tsakanin Rasha da Amirka cikin dan karamin lokaci, yana mai kuma jaddada yiwuwar su ma su bullo wa Amirka da wani salo na takunkumin.