Rikicin nukliyar ƙasar Iran | Labarai | DW | 23.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin nukliyar ƙasar Iran

Hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nukliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya, ta sake haɗuwa a birnin Vienna na ƙasar Austriyya, da nufin ci gaba da tantana rikicin nukliyar ƙasar Iran.

Shugaban hukumar, IAEA Mohamded Albaradei, ya yaba da haɗin kann da Iran ta bada, to saidai ya ce har yanzu da sauran rina kaba, wajen cimma burin da aka sa gaba na ciwo kann hukumomin Teheran domin suyi watsi da shirin mallakar makaman Nukleya.

Mahaurorin da wakilan IAEA su ka tabka sun bayyana babbar ɓaraka, inda Amirka da abokan ƙawacenta, ke buƙatar saka saban takunkumi ga Iran , a yayin da ƙasashe ´yan baruwanmu, bisa jagorancin Kuba ke nuna adawa da wannan mataki.