Rikicin Nuklera Korea ta Arewa | Labarai | DW | 14.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Nuklera Korea ta Arewa

Amurika ta yi kira ga Korea ta Arewa ta cika alƙawarin da ta ɗauka na rusa tashoshin ta na makaman nuklea.

Yau ne wa´adin ƙarshe, na alkawarin ke cikawa, wanda hukumomin Pyong Yang su ka ɗauka, ranar 13 ga watan Februabu, a lokacin tanttanawar birnin Pekin.

Saidai ya zuwa yanzu, Korea ta Arewa, ba ta alamar rufe wannan tashoshi, ta na zargin Amurika ta saɓa na ta alkawari, na cire takunkummin ƙudaden ta ta saka mata.

A wani jawabi da ya gabatar yau asabar, shugaban tawagar Amurika a wannan tantanawa, Christopher Hill, ya ce Amurika a shirye ta ke ,ta ɓalle takunkumin, da zaran Pyong Yang, ta nuna niyar rufe tashoshin ta, na Nuklea.

Yau ne a ka tsara komawa tebrin shawarwari, a birnin Pekin na ƙasar Sin,tsakanin ƙasashe 6, dake tantana wannan rikici, amma a wani mataki na ba zata wakilin Korea ta Arewa, Kim Kye-Gwan, ya ƙauracewa taron.