1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nuklear Korea ta Arewa

March 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuPV

Duk da tafiyar hawainiyar da ake fuskanta, wajen warware rikicin makaman nuklear Korea ta Arewa, shugaban tawagar Amurika a wannan tanttanawa Kristopher Hill, yabayana kyaukyawan fatan warware wannan baddaƙala, a yan kwanaki masu zuwa:

„Ina kyautata zaton mu na bisa kyaukyawar turba, kuma ƙila a yan kwanaki ƙalilan za mu juya baben wannan rikici, mu kuma shiga wata sabuwar haraka“.

Bayan yarjejeniyar da ka cimma, a watan februaru da ya gabata, na kawo karshen wannan taƙƙadama, a yau, shugaban tawagar Korea ta Arewa, a tantanawar ya hurta cewar,ƙasar sa, ba zata rufe tashoshin ta ba, na samar da makaman nuklea, mudun Amurika ba ta ɗage mata takunkumin karya tattalin arzikin ba.

Kim kye-Gwam ,ya zargi Amurika ta saɓa alkawarin da ta ɗauka, a lokacin yarjejeniyar watan da ya gabata.

Shima a nasa ɓangare, shugaban hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea, ta MDD, DR Mohamed El Baradei , bayan kammalla ziyara aikin sa a Korea ta Arewa, ya kyauttata zaton kawo ƙarshen taƙƙadamar, nan da wata mai zuwa.

Ranar litinin idan Allah ya kai mu, ƙasashe masu shiga tsakanin rikicin za su koma tebrin shawarwari a birnin Pekin na ƙasar Sin.