1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Nuklear Korea ta Arewa

July 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuHD

Hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta yi lalle marhabin da matakin da Korea ta Arewa ta ɗauka na amincewa da buɗe ƙofofin tashoshin ta, na samar da makaman nuklea, ga masu bincike na ƙasa da ƙasa.

Shugaban hukumar Mohamed Al Baradei, ya bayyana hakan, bayan rangadi da ya kai, a wannan ƙasa a makon da ya gabata.

Tun ranar 13 gab watan februaru na wannan shekara, hukumomin Pyong Yang su ka alƙawarta bada haɗin kai, amma su ka ci tuwan fashi.

A wani rahoto da ya gabatar yau talata, Mohamed Al Baradei ya bayyana cimma kyaukyawan sakamako a tantanawar da yayi da hukumomin Korea ta Arewa.

A ci gaba kuma da yunƙurin warware wannan takkadama, shugaba Kim Yong Il, ya gana a sahiyar yau,, da ministan harakokin wajen ƙasar Sin , Yang Jiechi.

Sin na cikin sahun ƙasashen da ke sappa da marwa, domin kawo ƙarshen wannan rikici.