Rikicin nuklear Korea ta Arewa | Labarai | DW | 11.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin nuklear Korea ta Arewa

Ƙurraru a game illimin nuklea,na ƙasar Amurika, sun fara rangadi a Korea ta Arewa, da zumar sa ido ga tashoshin nuklear da ƙasar ta mallaka.

A tsawan kwaniki 5, wannan massana za su binciki tashoshin, su kuma bayyana rahoto, a game da alƙawarin da hukumomin Pyong Yang su ka ɗauka, na dakatar da shirin mallakar nuklea.

A ckin wannan wata ne , a ka shirya komawa tebrin shawara tsakanin ƙasashen Amurika Japon Sin, Russia da Korea ta Arewa, da ta Kudu, a game da wannan batu, wanda aka jimma ana kai ruwa rana kan sa, tunshekara ta 2003.

A watan februaru na wannan shekara, a ka cimma yarjejeniya, wadda a sakamakon ta, Korea ta Arewa ta alƙawarta dakatar da shirin nuklea.

A tsakiyar watan Juli, ta rufe ɗaya daga manyan wannan tashoshi.