1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Nukiliyar Koriya ta arewa

Ibrahim SaniDecember 31, 2007
https://p.dw.com/p/CiJD

Rikicin Nukiliyar ƙasar Koriya ta arewa da alama, na ci gaba da ɗaukar sabon salo. Hakan ya biyo bayan gazawar ƙasar ne na bayar da cikakken bayanin shirinta na Nukiliya, kamar yadda tayi alƙawari a baya. A wannan rana ta yau 31 ga watan Disamba, Koriya ta arewa tayi alƙawarin aiwatar da wannan yarjejeniya. Tuni Amirka ta bayyana rashin gamsuwarta a game da wannan mataki na Koriya ta arewan. Matakin a cewar Amirka, abune da ka iya mayar da hannun agogo baya, game da shawo kan wannan rikici.. Rahotanni sun shaidar da cewa kin aiwatar da wannan yarjejeniya, abune da zai haifar da saƙalawa ƙasar takunkumi.