1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin nukiliyar kasar Iran

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvB3

A takaddamar da ake yi dangane da shirin nukiliyar Iran, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier yayi kira ga gamaiyar kasa da kasa da ta nemi hanyoyin diplomasiya don warware wannan rikici. A lokaci daya kuma ministan yayi gargadi game da yin wani tunanin daukar matakan soji. Maimakon haka kamata ya yi a bi hanyoyin diplomasiya don samun masalaha, inji ministan lokacin hira da wata tashar telebijin ta Jamus. Da farko dai gwamnatin Isra´ila ta yi barazanar daukar matakan soji, amma ministan tsaron ta Shaul Mofaz ya ce a halin yanzu kasarsa ta fi bawa hanyoyin diplomasiya fifiko. Duk da haka dai Isra´ila na zaman shirin ko-takwana idan kokarin warware wannan takaddama cikin lumana ya ci-tura. Iran dai ta sha nanata cewa shirin ta na nukiliya na samar da wutar lantarki ne amma ba makamai ba.