Rikicin nukiliyar kasar Iran | Labarai | DW | 10.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin nukiliyar kasar Iran

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce nan da makonni kadan masu zuwa kwamitin sulhun MDD ka iya zartas da wani kuduri akan shirin nukiliyar Iran da ake takaddama a kai. Rice ta fadawa tashar telebijin ta ABC cewa kafin wannan lokaci KTT zata gabatar da wani sabo tayi wanda zai bawa Iran ´yancin tafiyyar da shirin nukiliya don amfanin fararen hula. Rice ta ce hanya mafi dacewa ita ce a jira har tsawon makonni don warware wannan rikici ta hanyoyin diplomasiyya. Rice ta bayyana takardar da shugaban Iran mahmud Ahmedi-Nijad ya aikewa shugaba Bush da cewa ba ta matsayin wani sabon babi ga huldodin diplomasiya tsakanin kasashen biyu. A kuma halin da ake ciki kasar Indonesia ta yi tayin shiga tsakani don sulhunta rikicin nukiliyar Iran da gamaiyar kasa da kasa.