Rikicin nukiliyar kasar Iran na ci gaba da ruruwa | Labarai | DW | 15.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin nukiliyar kasar Iran na ci gaba da ruruwa

Faraministan Israel, Mr Ehud Olmert ya kara daukaka kira ga dangantakar kasa da kasa na daukar mataki kann iran, game da aniyar ta na mallakar makamin Atom.

Bugu da kari faraministan ya kuma bukaci kasashen larabawa, da suma su gaggauta daukar matakin yin Allah wadai da wannan aniya ta Iran.

Gaggauta daukar matakin dakile aniyar kasar ta Iran a cewar Mr Olmert ya zama wajibi, don kauce fadawa wani rikici, a yankin na gabas ta tsakiya.

Mr Olmert ya fadi hakan ne kuwa yayin da yake jawabi gaban taron shekara shekara, na kungiyyar bani yahudu dake arewacin Amurka.

A dai farkon wannan makon ne, Mr Olmert ya gana da shugaba Bush da kuma wasu jami´an Amurka, a game da rikicin nukiliyar kasar ta Iran.