Rikicin Nukiliyar Iran | Labarai | DW | 18.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Nukiliyar Iran

Kasar Iran ta lashi takobi na kin yin watsi da shirin ta na makamashin Nukiliya, duk da taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da ke cigaba da gudana domin duba yiwuwar sanyawa kasar takunkumi. Kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya ya gudanar da taro don duba sabobn daftarin kudiri da Faransa da Britaniya suka gabatar. Wannan dai na a matsayin matakin farko na kaiwa ga sanyawa Iran din takunkumi a dangane da takaddamar Nukiliyar. Iran ta nanata cewa ta na amfani da makamashin nukiliyar ne domin samar da hasken wutar lantarki, yayin da a hannu guda Amurka da sauran kasashen turai ke zargin kasar da yunkurin mallakar makamin kare dangi.