Rikicin Nukiliyar Iran | Labarai | DW | 25.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Nukiliyar Iran

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice ta ce, Amurka ta fi zabar hanyoyi na diplomasiya domin warware taƙaddamar nukiliyar Iran. A wani taron manema labarai da ta gudanar tare takwaranta na ƙasar Girka Dora Bakoyannis a birnin Athens, Condoleezza Rice ta baiyana cewa kalamai na baya bayan nan da shugaban ƙasar Iran ya yi, na kara nesanta kasar ne daga gamaiyar ƙasa da ƙasa. A daura da ziyarar sakatariyar harkokin wajen Amurkan zuwa ƙasar Girka, yan sandan kwantar da tarzoma sun yi ta harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa ɗaruruwan jamaá da suka yi dandazo inda suka nufi ofishin jakandancin Amurkan a birnin Athens domin nuna adawa da ziyarar ta a ƙasar. Masu zanga zangar sun rika jifa da duwatsu yayin da suke ƙoƙarin karya shingen da yan sanda suka gindaya. Condolezza Rice za kuma ta ziyarci ƙasar Turkiya kafin ta wuce zuwa Bulgaria inda zata gana da ministocin harkokin waje na ƙungiyar tsaro ta NATO: