Rikicin nukiliyar Iran | Labarai | DW | 02.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin nukiliyar Iran

Manyan jamián kasashe biyar masu wakilcin dundundun a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na gudanar da taro yau a birnin Paris domin daukar mataki na bai daya na game da bujirewar kasar Iran na kin dakatar da shirin ta na makamashin nukiliya. Taron dai shi ne na farko a tsakanin kasashen biyar wadanda suka hada da Britaniya da China da Faransa da Rasha da kuma Amurka tun bayan da hukumar majalisar dinkin duniya mai lura da hana yaduwar makaman nukiliya IAEA ta gabatar da Iran ga kwamitin sulhun majalisar dinkin duniyar a dangane da keta dokar majalisar dinkin duniyar tare kuma da kin amincewa ta dakatar da bunkasa sinadarin Uranium. Amurka da Britaniya da kuma Faransa wadanda ke baiyana shakku cewa Iran na fakewa ne da shirin samar da makamashi domin kera makamin kare dangi, sun zafafa kaimi na daukar tsauraran matakai a kan Iran wanda ya hana da kakaba mata takunkumi. A waje guda kuma kasashen Rasha da China na yin baya baya wajen kaiwa ga daukar wannan mataki inda suke kokarin nemo hanyoyi na diplomasiya domin shawo kan Iran ta bi umarnin gamaiyar kasa da kasa dangane da shirin nukiliyar. A wata ganawa ta wayar tarho, Shugaban Amurka George W Bush ya baiyanawa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin muhimmancin hana Iran mallakar makamin nukiliya.