Rikicin makomar Kosovo | Labarai | DW | 11.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin makomar Kosovo

Ƙasar Serbia ta ce zata bukaci komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya nemi shawarar kotun ƙasa da ƙasa kan batun aniyar Kosovo ta aiyana yancin kanta. A halin da ake ciki kuma wani mai magana da yawun shugabannin Albaniyawan Kosovo ya faɗawa manema labarai a birnin Pristina cewa zasu aiyana yancin kansu kafin watan Afrilu na shekara mai zuwa .Sanarwar ta zo ne bayan ƙarewar waadin Majalisar Dinkin Duniya na kammala cimma yarjejeniya kan makomar Kosovo. Amurka da mafi yawancin ƙasashen turai sun ce zasu amince da yancin Kosovo. Sai dai kuma Rasha tace bai dace a bar Kosovo ta ɓalle ba tare da amincewar Serbia ba.