1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin makaman nuklear Iran

A yayin da ya rage kwanaki 2 rak, a zo ƙarshen wa´adin da komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, ya ba Iran, na yin watsi da batun nukleya, har yanzu hukumomin Teheran, sun yi tsawuwar gwamen jaki, a dangane da manufofin su.

Saidai Iran ta bayana niyar ci gaba, da shawarwari da ƙasashen da ke shiga tsakini, a cikin wannan rikici.

A yau talata ministan harakokin wajen France ,Philips Duzte –Blazy, ya ce France na goyan baya Iran, a kan batun komawa tebrin shawawari, duk da cewar, ta na kuma buƙatar ganin Iran ɗin, ta bi umurnin Majalisar Dinkin Dunia.

A nasa ɓangare, sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayyar turai, Javier Solana, ya ambata shirya taro, na mussamman, kamin ƙarshen wannan wata, da zai haɗa tawagar Iran, da ta ƙasashen EU.

A hira da yayi yau ,da manema labarai,shugaban ƙasar Iran, Mahmud Ahmadinedjad,ya gayyaci shugaba Bush na Amurika, zuwa mahaurar ƙeƙe da ƙeƙe, ta hanyar gidan talbajan, a game da siyasar dunia.