Rikicin makaman nuklear Iran | Labarai | DW | 20.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin makaman nuklear Iran

Kantoman kungiyar Tarayyar Turai kan manufofin ketare, Javier Solana zai gana da babban mai shiga tsakani akan harkokin nukiliyan Iran, Ali Larjani, ranar laraba mai zuwa. Sanarwa daga Brussels, tace shugabannin, zasu yi anfani da wannan dama wajen duba yiwuwar sake komawa kann teburin shawara a game da mallakar makamashin nukiliya na Iran. Har yanzu dai ba’a riga aka tattance magana akan wurin zaman taron nasu, bayan da wata kafa ta yada labaran Iran ta sanar cewar a jiya alhamis ne shugabannin suka amince da saduwa ta wayar tangaraho