Rikicin makaman nuklear Iran | Labarai | DW | 01.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin makaman nuklear Iran

Kasar Iran, ta bayyana aniyar komawa tebrin shawarwari tare da hukumar yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea ta MDD.

Ta bayyana hakan, a sakamakon ganawar da aka yi jiya, tsakanin sakataran harakokin wajen ƙungiyar gamayya turai Havier Solana, da kuma shugaban tawagar Iran a tanttanawar rikicin nuklea Ali Larijani.

Solananya bayyana gamsuwa, a game da ci gaban da aka samu a wannan badaƙala.

Idan dai ba a manta ba, ƙasar Iran ta yi tsayuwar gwamen jaki, a game da buƙatocin Majalisar Ɗinkin Dunia na ta yi watsi da aniyar mallakar makaman nuklea.

Tawagogin 2, sun yanke shawara sake gamuwa, nan da makwani 2 masu zuwa, domin ci gabada tantanawa.

Saidai a yayin da ta ke maida martani, sakatariyar harakokin wajen Amurika, Condoleesa Rice, ta ce, ci gaban da a ka ce an samu a taron na jiya, irin na mai haƙar rijiya ne.