1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin lardin Darfur

Mdd da kungiyar gamayyar Afrika sun sanar da sabbin tsare tsare na samarda zaman lafiya a yankin Darfur,mai fama da rikici ya ayankin yammacin Sudan.Jakadan Mdd na musamman a Darfur Jan Eliasson,zai kai rangadin aikiyankin,da nufin dakatar da fada tsakanin dakarun yan adawa dana gwamnati,dake cigaba da gwabza fada.A yanzu hakan dai mdd na kokarin fadada yawan dakarun kiyaye zaman lafiya a yankin,amma har yanzu ana fuskantar da sabani da gwamnatin Sudana dangane da adadin dakarun da zaa tura.A shekaru 4 da suka wuce dai,an kiyasta cewa mutane akalla mutane dubu 200 suka rasa rayukansu a lardin na Darfur.Duk kuwa da yarjejeniyar sulhu da aka cimma awatan mayun daya gabata,tsakanin gwamnatin kasar da daya daga cikin manyan kungiyoyin adawan yankin,ana cigaba da fada da kungiyoyin da suka ki rattaba hannu a yarjejeniyar.