1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin lardin Darfur

Duk da lafawan hare haren yan tawaye a lardin darfur dibn kasar Sudan,ana cigaba da gasawa mata aya a hannu ta hanyar cin zarafinsu.Ayau ne akayiwa wata mace mai shekaru 25 da haihuwa fyade a gaban yayanta guda biyu,wadanda suka tsorata a harin da aka kai musu.Matan Darfur din dai nacigaba da rayuwa cikin irin wannan mawuyacin hali na kunya da tsoron yadda alumma zata rika kallonsu.Matar wadda taki ambatan sunanta .ta hakikance cewa wani jamiin sojin gwamnati dauke da bindiga ne yayi mata fyade,bayan fada mata cewa maigidanta ya barta domin zuwa fada da yan adawa.A yanzu haka dai wannan baiwar Allah na cikin mawuyacin hali na jinya sakamakon fyaden da akayi mata,inda tace har yanzu ta kasa fada mijinta.Rahotanni mdd sunyi nuni da yadda ake kulle irin wadannan mata da akanyi musu fyade,akan laifin cin mutuncin Aure,al halin ba laifinsu bane.