1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin " l´Arche de Zoe"

Yahouza Sadissou MadobiNovember 9, 2007
https://p.dw.com/p/C9qq

Haɗin gwiwar ƙungiyoyin bada agaji a yankin Darfur na ƙasar Sudan, sun bayyana sanarwar haɗin gwiwa, wace a cikin ta, su ka yi Allah wadai da takwarar su l Arche de Zoe ta kasar France.

Idan dai ba a manta ba, a watan da ya gabata a ka kama wannan ƙungiyar bada agaji, da lefin yunƙurin satar ƙananan yara.

Ƙungiyoyin sun bukaci a bambamta ɗanyan aikin L´Arche de Zoe da ayyukansu na tallafawa jama´a, matsugunan yan gudun hijira na Darfur da ke ƙasar Tchad.

A dangane da wannan rikici, hukumomin ƙasar France, sun yi lale marhabin da hukunci da kotu ta yanke, a yau, na yin belin yan ƙasar Spain 3 da kuma mutum ɗaya na ƙasar Belgium.

A yammacin yau ne, sakataran harakokin wajen ƙasar Spain, ya je takanas birnin N´Djamena, inda ya tafo da spaniyawan 3 da aka sallama.

Ministan yayi godiya ga hukumomin ƙasar Tchad da su ka amince da belin mutanen, sannan ya alƙawarta cewar Spain zata ɗaukar yaunin karatun yaran103 baki ɗaya.