1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kyrgyzstan da yanayin rayuwar al'uma

June 19, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da gidauniyar taimakawa yan gudun hijira a Kyrgyzstan

https://p.dw.com/p/NxHK
Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki-moonHoto: AP

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar shelar taimakon jin ƙai na tsabar kuɗi Dala miliyan 71 domin taimakawa dubban ɗaruruwan mutanen da rikicin ƙabilanci ya ritsa da su a Kyrgyzstan. Tun da farko Amirka ta baiyana halin da ake ciki a kudancin Kygyzstan da cewa ya shiga wani yanayi na taɓarɓarewar halin rayuwar al'uma. Babban jakadan Amirka a yankin kuma mataimakin sakataren harkokin waje Robert Blake ya yi kiran gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa ga rikicin ƙabilancin bayan da ya ziyarci sansanonin da aka tsugunar da yan gudun hijirar a maƙwabciyar ƙasar Uzbekistan.

Kirgisistan Kirgisien Khirgistan Kyrgyzstan Flüchtlinge Lager Flash-Galerie
Yan gudun hijira yan ƙabilar UzbekHoto: AP

Kimanin mutane 400,000 ne yan ƙabilar Uzbek suka yi ƙaura daga yankunansu.

Shugabar gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Kyrgyzstan Rosa Otunbayeva ta kai ziyara wasu birane a gundumomin Osh da Jalalabad dake kudancin ƙasar domin kwantar da hankulan al'uma. Otunbayeva ta ce yawan mutanen da suka rasu a sanadiyar rikicin sun tasamma mutum 2,000  wanda ya ninka adadin da aka baiyana a baya har sau goma.

Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala

Edita : Halima Balaraba Abbas