Rikicin kwango ya ritsa da sojan Ghana ɗaya
April 4, 2010Wani sojan Ghana da ke aikin kiyaye zaman lafiya a Jamhuriyar Demokaraɗiyar Kwango ya rigamu gidan gaskiya, a lokacin taho mu gama tsakanin dakarun gwamanti da kuma mayaƙan sa kai. Dakarun na Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kwango sunyi musayar wutan ne da mayakan ƙabilanci kimanin 100, a garin Mbandaka da ke arewa maso gabashin ƙasar , yankin da aka fuskanci rikicin ƙabilanci a bara. Rikicin dai ya ɓarke ne bayan da jami'an tsaro suka gano kwale-kwalen dake ɗauke da 'yan adawan da aka yi jigilarsu daga birnin Kinshasa i zuwa wannan yanki.
Ministan cikin gida wato Guy Inenge, ya nunar da cewa ya zuwa yanzu yan bindiga daɗin, sun tsere zuwa cikin ƙauyuka dake yankin. A watan Oktoba ne dai rikici ya ɓarke tsakanin ƙabilun Lobala da kuma Monzaya, tare da haddasa mutuwan mutane 270, a yayinda aka tilastawa wasu dubu 187, barin matsugunnensu.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala