Rikicin Kirgistan ya sake yin muni | Labarai | DW | 12.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Kirgistan ya sake yin muni

Gwamnatin Kirgistan ta baiwa sojoji lasisin yin kisa a yankin Osh

default

Gwamnatin ƙasar Kirgistan ta umarci dakarun ƙasar da su yi harbi - har lahira duk wanda suka gani a yankunan da suka kafa dokar ta ɓaci dake kudancin ƙasar. Wata dokar da hukumomin ƙasar suka amince da ita dai, ta tanadi cewar za'a ci gaba da yin aiki da wannan umarnin ne har lokacin da gwamnatin wucin gadin ta cire dokar ta ɓacin, domin a cewar ta, hakan zai bada kariya ga fararen hula da kuma su kansu dakarun ne daga masu tada ƙayar baya. A halin da ake ciki kuma, hukumomin Rasha sun sanar da cewar, ba za su tura dakaru domin taimakawa kwantar da hankalin jama'a a rikicin daya sake ɓarkewa a yankin kudancin ƙasar Kirgistan ba, amma kakakin shugaban Rasha Dmitry Medvedev, ya bayyana cewar, Rasha za ta aike da kayayyakin agaji zuwa ƙasar. Shugabar wucin gadin ƙasar ta Kirgistan Roza Otunbayeva, ta yi na'am a wannan Asabar da cewar, gwamnatin ta rasa ikon da take dashi a birnin Osh, wanda shi ne na biyu mafi girma a ƙasar. Faɗan daya sake ɓarkewa a ranar Jumma'ar nan tsakanin dakarun gwamnati da kuma mayaƙan ƙabilar Uzbek, ya yi sanadiyyyar mutuwar aƙalla mutane 77, a yayin da wasu 1000 kuma suka sami rauni. An cinnawa galibin birnin wuta, kana da dama daga cikin shagunan sayar da kayayyaki ko dai an fasa su ko kuma suna rufe, lamarin daya janyo matsalar ƙarancin abinci. Wannan rikicin dai, shi ne mafi muni - tun sa'adda aka hamɓarar da gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Kurmanbek Bakiyev, yayin wani juyin mulkin da aka zubar da jini cikin watan Afrilun da ya gabata. Ana kuma fargabar cewar, tashin hankalin ka iya yaɗuwa zuwa wasu sassa na yankin tsakiyar Asiya. Yankin dai na da arziƙin man fetur da iskar gas, kana yana da muhimmancin gaske ta fannin tattalin arziƙi ga Rasha, da kuma sauran ƙasashen yammacin duniya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Yahouza Sadisou