Rikicin kasar Sri Lanka | Labarai | DW | 06.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Sri Lanka

An bude wuta akan dakarun gwamnatin Sri Lanka a arewacin kasar a daidai lokacin da wakilin Japan Yasushi Akashi ya sauka a tsibirin a wani yunkuri da ake yi baya bayan nan da nufin hana barkewar yakin basasa a kasar. An kai musu harin ne a garin Jaffna dake hannun dakarun gwamnati. A jiya rundunar sojin kasar ta ce ta lalata wani kwale-kwale da ´yan tawaye suka so yin amfani da shi wajen kai harin kunar bakin wake da kuma wata babbar mota cike da makamai. Dukkan bangarorin biyu sun nuna shirin komawa kan teburin shawarwarin zaman lafiya to amma jami´an diplomasiya na fargabar cewa kasar ka iya sake fadawa cikin yakin basasa. A yau wakilin na Japan ya sauka a birnin Colombo, inda zai gana da shugaba Mahinda Rajapakse da shugaban bangaren siyasa na kungiyar Tamil Tigers S.P. Thamilselvan a ranakun litinin da talata.