Rikicin kasar Sri Lanka ya yi muni | Labarai | DW | 17.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Sri Lanka ya yi muni

Wani kazamin fada ya barke tsakanin dakarun gwamnati da ´yan tawayen kungiyar Tamil Tigers a Sri Lanka. Wani kakakin rundunar sojin kasar ya ce jiragen saman yakin gwamnati da jiragen yaki na ruwa sun kai hare hare akan sansanonin ´yan Tamil Tigers bayan wani hari da ´yan tawayen suka kai kan wani caji ofis da kuma barikin sojin ruwa dake arewa maso yammacin kasar. Akalla mutane 24 ciki har da dakarun tsaro da kuma ´yan tawaye suka rasa ransu a gumurzun da aka gwabza a yankin. ´Yan tawayen sun kai harin ne don mayar da martani ga farmakin da sojoji suka shafe kwanaki biyu suna kaiwa akan garin Kilinochchi, cibiyar ´yan kungiyar Tamil Tigers. An kuma ba da rahoton fashewar wani abu mai karfin gaske a wannan yanki dake arewa da babban birnin kasar.