1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Kasar Somalia

Gwamnatin Somalia ta rufe gidajen radiyo masu zaman kansu guda uku cikin kwanaki 2, yayin da rikici ke cigaba tsakannin sojojin gwamnati masu samun taimako daga Habasha a rikinta da dakarun kungiyoyin Islama a birnin Mugadishu. An rufe gidajen Radiyo Simba da Banadir a yau talata, bayan shi gidan radiyon Sabelele ta samun umurnin ta dakatar da watsa shirye-shirye daga gwamnati tun jiya litinin. Dukan gidajen radiyon guda uku na birnin Mogadishu, inda dakarun Habasha, suka kaddamar da farmaki, bayan an kashe daruruwan sojojinta kuma aka nakasar da wasu tare da jan wasu kann tituna, a ranar alhamis da ta gabata.