Rikicin kasar Somalia | Labarai | DW | 11.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Somalia

Dubun dubatan mutane na tserewa daga Mogadishu babban birnin kasar Somalia yayin da ake ci-gaba da gwabza kazami fada mafi muni a cikin wannan shekara. Yanzu haka dai yawan wadanda aka kashe a artabun da aka shafe kwanaki ana yi tsakanin dakarun Ethiopia dake goyawa gwamnatin Somalia baya da sojojin sa kai na ´yan Islama ya kai mutane 80. A jiya asabar an dan samu kwarkwaryar kwanciyar hankali a babban birnin wanda yaki ya yiwa kaca-kaca. Likitoci sun ce suna fama da matsaloli wajen kula da mutanen da suka jikata saboda karanci magunguna da rashin gadaje a asibitoci.