Rikicin kasar Somalia | Labarai | DW | 01.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Somalia

Ana cigaba da lugudan wuta da aman boma bomai cikin tsakiyar birnin Mogadisho din kasar somalia,kuma hukumomin Uganda sun sanar da kashe jamiin sojinsu guda, ayayinda aka shiga rana ta hudu a mummunar fada data barke tsakanin hadin gwiwan dakarun habasha da Somaliyan ,da mayakan sakai na wannan kasa.

Tun da rahotanni dake nuni dacewa shugabannin hauloli dake fada a bangaren mayakan sakai,sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da dakarun Habasha,wanda ke zama na biyun irinsa,har yanzu ana cigaba da saran rayuka musamman na fararen hula,sakamakon wannan arangama dake ci gaba da gudana tsakanin bangarorin,wanda kuma kasashen duniya suka nuna damuwa akai,kamar yadda jakadan Amurka wa kasar Kenya Michael Rannbeger ya nunar.

Yace babu shakka Amurka tana cikin matukar damuwa dangane da matsayin wannan tashin hankali.

Ko da yake abunda keda muhimmanci shine duk da wannan fada dake cigaba da gudana,alummomin somaliyan basu taba samun dama makamancin wannan ba na cimma sasanta tsakaninsu .