Rikicin kasar Nepal | Labarai | DW | 08.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Nepal

An kashe ´yan tawayen Mawo-ist guda 9 da kuma jami´an tsaro 3 a tashe tashen hankula da suka wakana cikin daren jiya a fadin kasar Nepal. Hakan dai ya zo ne a daidai lokacin da kasar ke fama da yajin aiki na gama gari da masu fafatukan neman mulkin demukiradiya suka shirya. Wata sanarwa da sojin kasar ta bayar ta ce dubban ´yan tawaye sun kai hare hare a lokaci daya akan sansanonin jami´an tsaro da kuma ofisoshin gwamnati a biranen Rupandehi da Kapilbastu. A kuma halin da ake ciki gwamnati ta kafa dokar hana fita da rana a birnin Kathmandu, inda ta yi gargadin cewa ´yan sanda zasu harbe duk wanda ya ki bin wannan doka. Mazaunma birnin sun ce an katse hanyoyin sadarwa na wayoyin salula da kuma intanat.