Rikicin kasar Jojiya | Labarai | DW | 08.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin kasar Jojiya

Shugaban ƙasar Jojiya Mikhail Sakashvili ya kafa dokar ta ɓaci a faɗin ƙasar na tsawon makwanni biyu sakamakon cigaban arangama tsakanin jamián tsaro da dubban masu zanga zanga. Firaministan ƙasar Zurab Nogaideli yace an yi ƙoƙarin kawar da yunƙurin juyin mulki. Shugaba Sakashivili ya zargi waɗanda ya kira yan koren ƙasar Rasha da haddasa tarzomar yana mai cin alwashin korar jakadun ƙasar ta Rasha waɗanda yace suna aikin leken asiri a cikin ƙasar sa. Hukumomin lafiya sun ce a ƙalla mutane fiye da 500 waɗanda su ka sami raunuka a yayin zanga zangar aka yi wa magani, yayin da wasu mutanen kimanin ɗari ɗaya su ke kwance a Asibiti sakamakon duka da kulake da kuma barkonon tsohuwa da yan sanda su ka harba musu domin tarwatsa zanga zangar. A halin da ake ciki kuma gwamnatin ta rufe dukkanin kafofin yada labarai masu zaman kan su da ke cikin ƙasar.